0 Comments

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bukaci da a rika daukar tsastsauran hukunci kan wadanda ke cin zarafin ‘ya’ya mata da kananan yara.

Osinbajo ya yi wannan jawabi ne a dakin taro na Banquet da ke fadar shugaban kasa ta Aso Rock a Abuja a jiya Asabar, wajen wani taro da ofishin mai dakin shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ya shirya.

Mataimakin shugaban kasar wanda ya bukaci da a sake nazartar dokokin cin zarafin ‘ya’ya mata da kananan yara saboda nakason da dokar ke da ita, ya ce yin hakan ne kawai za a magance da yawa daga cikin matsaloli da ake fuskanta.

Farfesa Yemi Osinbajo ya kuma bayyana damuwar-sa kan yadda wasu matasan kasar nan ke rasa rayukan-su a tekun Baharrum, a yunkurin da suke na neman tsallakawa nahiyar turai, haka zalika ya kuma ce ba daidai bane a rika bautar da kananan yara ta hanyar yin aikatau a gidaje  da kuma yin bara.

Ana ta bangaren mai dakin shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari, ta yi kira ga iyalan wadanda aka ci zarafin-su da su rika sanar da jami’an tsaro a duk lokacin da lamarin ya faru domin daukar mataki.

Share
Share
Language »