0 Comments

A yau ne za’a fara gasar kungiyoyi Shida anan Kano domin share fagen fara gasar firimiyar ta shekarar badi.

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ce za ta fara wasa da kungiyar Enyimba da misalin karfe daya na rana a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata.

Haka zalika Akwa united za ta fafata da Plateau united, yayin da Kungiyar Super Eagles ta ‘yan wasan cikin gida wato CHAN Eagles za ta barje gumi da MFM FC dukkan-nin wasannin za a yi su ne a filin na Sani Abacha da ke Kofar Mata a nan Kano.

Share
Share
Language »