Freedom Radio Nigeria Labaran Jihar Kano Gwamnatin Najeriya ta sanar da ranakun 25 da 26 ga watan Disamba a matsayin ranakun hutu

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ranakun 25 da 26 ga watan Disamba a matsayin ranakun hutuGwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da ranakun 25 da 26 ga watan Disambar da muke ciki da kuma ranar 1 ga watan Janairu mai kamawa a matsayin ranekun hutu a fadin kasar nan.

Gwamnatin ta bada hutun ne domin bukuwan kirsimeti da kuma na sabuwar shekara mai kamawa ta 2018.

Babban sakatare a ma’aikatar harkokin cikin gida ta tarayya Abubakar Magaji ne ya bada sanarwar a birnin tarayya Abuja.