0 Comments

Hukumar kula da gidajen yari ta kasa ta ce mutane hudu ne suka rasa rayukan-su yayin wani yunkurin tserewa da wasu fursunoni su ka yi a gidan yarin Ikot Ekpene da ke jihar Akwa Ibom.

A cewar hukumar a jiya Laraba ne wasu fursunoni a gidan yarin suka farwa wasu jami’an hukumar da ke aiki a dakin girkin gidan yarin.

Hukumar ta kuma ce ba ya ga wadanda suka tseren wasu fursunoni 36 kuma sun tsere daga gidan yarin.

Kwanturola Janar na hukumar gidan yarin reshen jihar Akwa Ibom Alex Oditah, ya shaidawa manema labarai cewa, hukumar ta samu nasarar kama wasu mutum bakwai daga cikin fursunonin da suka nemi tserewa, yayin da wasu 36 har yanzu ba akai ga gano inda suke ba.

A cewar Alex Oditah, tuni bincike yayi nisa domin gano musabbabin faruwar lamarin.

Share
Share
Language »