Hukumar EFCC ta damke tsohon shugaban hukumar ilimin bai daya ta kasa

Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ce ta damke tsohon shugaban hukumar ilimin bai daya na kasa Malam Sulaiman Dikko bisa zargin sa da almundahanar Naira biliyan 20.

Haka kuma hukumar ta damke wasu yan kwangila da wasu manyan daraktocin hukumar ta UBEC da ke kula da sha’anin kudi a hukumar da hannu cikin badakalar.

Haka kuma hukumar ta kwace fasfunan Sulaiman dikko da sauran wadanda ta damke domin kada ta samu tsaiko wajen binciken da take yi a kansu.

Wata majiya ta shaidawa manema labarai cewar daga cikin abida ake bincikar su har da batun wasu kudden da aka warewa hukumar ilimin bai dayan, da makarantun hadaka na gwamanti sai dai an karkatar da su zuwa wasu lamarin daban.

Badakalar ta hadar da ta biliyan ashirin wadanda aka ware domin siyan kayan koyar da karatu a makarantun kimiyya da fasaha na gwamnati tarayya da kuma litttafan shirin muradun karni da aka siyo domin rarrabawa a makarantun hadaka na gwamanti 104 a fadin kasar nan.

Share
Share
Language »