Wakilan Kamfanin samar da man fetur da hukumar DPR suna ci-gaba da ziyarar bazata don bankado masu boye mai

Wakilai daga Kamfanin samar da man fetur na Najeriya da kuma hukumar kula da albarkatun man fetur DPR karkashin jagoranci shugaban Kamfanin Maikanti Baru sun ci gaba da kai ziyarar bazata gidajen mai a birini tarayya Abuja domin bankado masu boye mai da gan-gan.

Hukumomin na kai ziyarar ne tare da taimakon hukumar tsaro ta Civil Defence domin tabbatar da cewa an dai-daita tsayuwar gidajen man da ke sayar da mai akan Naira 250 a maimakon naira 145 da gwamnati ta kayyade.

Haka kuma mai Kanti Baru ya bada umarnin rarrabawa mutane man da aka samu a gidajen man da suke sayar wa sama da farashin gwamnati kyauta, a wani bangare na hukunta masu sayar da man da tsada.

Mai Magana da yawun shuganan Kamfanin man na NNPC Ndu Ughamadu ya shaidawa manema labarai a jiya cewar, umarnin da fadar shugaban kasa ta bayar ga Kamfanin da kuma jami’an tsaro domin kawo karshen matsalar karancin man fetur din da ake fama da shi, inda ya ce nan da yan kwanaki al’ummar kasar nan za su dara.

Haka kuma a jiya ne dai Kamfanin man na kasa NNPC ya ce ya dakatar da aikewa da mai babbar tashar sa da ke jihar Legas sakamakon gobarar da ta tashi a kusa da wurin.

Share
Share
Language »