Hukumar NBC ta gargadin kafafen yada labarai kan yada kalaman batanci

A yayinda babban zaben shekarar 2019 ke cigaba da kusantowa, hukumar lura da kafafen yada labarai ta Najeriya NBC ta gargadin kafafen yada labaran kasar da su nesanta kawunan su wajen yada kalaman batanci.

A cewar hukumar duk kafar yada labaran da aka samu musamman ma gidajen Rediyo da na Talabijin, to shakka babu zasu fuskanci fushin hukumar.

Shugaban hukumar na kasa Malam Modibo Ishaq Kawu ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi yayin wani taron karawa juna sani da kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Kwara ta shirya, wanda aka gudanar a birnin Ilorin.

Taron mai taken zamantar da harkar yada labarai, ya mayar da hankali ne kan irin rawar da kafafen yada labarai ke takawa a kasar nan.

Malam Modibo Ishaq Kawu ya bayyana cewa hukumar ta NBC ba zatayi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wata kafar yada labarai da aka samu da karya dokar da aka gindaya musu, musamman ma kan batun yada kalaman batanci.

Shugaban hukumar ya kuma yi Allah wadai kan yadda wasu kafafen yada labaran kasar nan ke yada kalaman batancin, wanda ya bayyana a matsayin wani yunkurin na tayar da zaune tsaye.

Share
Share
Language »