karin kudaden ganin likita da na sayan kati ya faru ne sakamakon matsalar tattalin arziki-AKTH

Hukumomin Asibitin koyarwa na Aminu Kano, da ke nan Kano AKTH sun bayyana  cewar karin kudaden ganin likita da da kuma karin kudin sayen kati da aka samu a asibitin ya faru ne sakamakon matsalar tattalin arziki da ake fama da ita a Najeriya.

Jami’in hulda da Jama’a na Asibitin Malam Aminu Inuwa ne ya bayyana haka a Juma’ar nan jim kadan bayan kammala shirin ‘Barka da Hantsi’ na nan tashar Freedom Radio.

Malam Aminu Inuwa, ya ce karin kudin da aka samu, ko kadan ba ya nufin matsantawa ga al’umma ba ne, illa iyaka yadda al’amura suka sauya a wannan lokacin na tsadar kayayyakin aiki.

Haka zalika ya kuma yi kira ga Jama’a da su rika kai koken su ga hukumar da ke da alhakin kula da korafi na asibitin, musammam ma idan aka samu rashin jituwa tsakanin jami’an jinya da marasa lafiya, inda kuma ya bukaci Jama’a da su kiyaye da daukar doka a hannu.

Ya kuma yi kira da jama’a da su yi hakuri da wannan sauyi da aka samu inda ya ce na dan wani lokaici ne, da zarar komai ya dai-daita al’amura za su koma yadda suke a baya.

Share
Share
Language »