yan Najeriya 6,672 sun dawo gida daga libiya a cikin wannan shekara

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta ce kawo yanzu yan Najeriya 6,672 ne suka dawo gida dan radin kansu daga libiya tun daga watan janairun farkon wannan shekara zuwa watan Disambar da muke ciki.

Shugaban hukumar ta NEMA Mustapha mai Hahaja ne ya bayyana haka lokacin da yake karbar wasu sabbin wadanda suka komo nan gida Najeriya su 257 daga kasar ta Libya.

Haka kuma Maihaja ya yaba da kokarin hukumar kula da yan gudun hijira ta duniya IOM bisa kokarin da ta ke yi na kwaso al’ummar da ke kasar ta libiya duk da cewa anan tsaka da gudanar da bukukuwan karshen shekarar a kasshe daban daban.

Shugaban wanda ya samu wakilicin jami’in hukumar mai kula da kudo-maso yammacin kasar nan Sulaiman Yakubu ya bukaci wadanda suka suka komo da su hada hannu da dukkanin hukumomin gwamnati domin shawo matsalar safarar mutane zuwa ketare.

Ya kuma buka ce su da su tallafawa gwamanti wajen gano masu mummmunar ta’adar safarar mutane wadanda ke yaudarar al’ummar kasar nan, ta hayar yi musu alkawuran rayuwa mai nagarta a kasshen Turai.

Inda yayi musu alkawarin gwamnati za ta yi amfani da dukkan bayanan da suka bata a cikin sirri ba tare da fallasa wadanda suka bada bayanan ba.

Share
Share
Language »