kotu ta daure babban sakatare shekaru 7 a gidan yari

Wata babbar kotun jihar Katsina ta yankewa tsohon babban sakatare a ofishin mataimakin gwamnan jihar Sule Yusuf Saulawa hukuncin daurin shekaru bakwai, ba tare da zabin tara ba, sakamakon samun sa da laifin zargin sa da aikata laifin badakala.

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa ce ta mika wanda ake zargin gaban kotu, ta hannun lauyan ta mai suna barista Sa’ad Hanafi, biyo bayan korafin da shugaban kamfanin Many Agro-Allied Chemical Musa Baba ya shigar gaban ta.

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin tsohon babban sakataren gwamnatin jihar ne karbar naira miliyan biyu da dubu dari biyar daga hannun Musa Baba domin taimaka masa wajen samo masa kwangilar takin da za’a sayarwa kananan hukumomin jihar.

Da yake yanke hukunci alkalin kotun mai shari’a Sanusi Tukur yace sakamakon shaidun da aka gabatarwa kotun da ke nuni da cewar wanda ake zargin ya aikata laifin da ake tuhumar sa da shi, ya yanke masa hukuncin zaman gidan kaso har na tsawon shekaru bakwai.

Share
Share
Language »