Hukumar kula da kididdigar ma’adinai ta bukaci a binciki kamfanin NNPC

Hukumar kula da kididdigar ma’adinai ta Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta binciki kamfanin mai na NNPC kan yadda ya yi da sama da Dala biliyan goma sha shida da miliyan dari takwas cikin ribar da ya samu, tun lokacin da aka kafa kamfanin fara samar da iskar gas a shekara ta 2000.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin rahoton binciken kamfanonin iskar gas da kuma mai na shekarar 2015 da ta fitar a juma’ar nan.

Rahoton hukumar ya kuma bayyana cewa an samu raguwar samun kudaden shiga a bangaren na mai da kuma iskar gas a shekarar 2015, idan aka kwatanta da shekarar 2014.

Babban sakataren hukumar ta NEITI Waziri Adio ya bayyana cewa rahoton da hukumar ta fitar na nuni da cewa akwai kudaden da ya kamata a bankado daga hannun wasu daga cikin hukumomin gwamnati, bayaga bullo da wasu hanyoyi da za’a yi wajen dakile badakalar kudade.

A cewar sa binciken da hukumar tayi na shekarar 2014 an samu kudin shiga ta bangaren mai da kuma iskar gas da ya kai sama da dala biliyan hamsin da hudu, amma rahoton shekarar 2015 an samu raguwar samun kudaden shiga a bangaren, la’akari da cewar an samu sama da dala biliyan 24.

Share
Share
Language »