‘yan Najeriya baza su shiga sabuwar shekara da wahalar man fetur ba-Maikanti Baru

Shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC Maikanti Baru ya tabbatar wa al’ ummar Najeriya cewa ba za su shiga sabuwar shekarar 2018 ana wahalar man fetur ba.

Maikanti Baru ya bayyana hakan ne Juma’ar da ta gabata a Abuja, inda ya jaddada matsayar kamfanin man na NNPC wajen ganin cewar farashin mai ya tsaya akan naira 145 akan kowance lita.

Ya kuma ce dukkan wani dillalin mai da aka samu da boye mai ko kuma sayar da shi sama da farashin da gwamnati ta kayyade zai fuskanci fushin hukuma.

Ya kuma ce kawo yanzu an fara samun saukin layin man da a ke fama da shi a birnin tarayya Abuja, inda ya ce nan ba da dadewa ba za daina samun cunkoso a gidanjen mai a fadin Najeriya.

 

Share
Share
Language »