Freedom Radio Nigeria Labaran Wasanni Najeriya zata doke kasar Argentina a gasar cin kofin duniya-Alex Iwobi

Najeriya zata doke kasar Argentina a gasar cin kofin duniya-Alex IwobiDan wasan Najeriya mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Alex Iwobi ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Najeriya zata doke takwararta ta Argentina a gasar cin kofin duniya wanda za’a yi a kasar Rasha tsakanin watan Yunin da Yulin shekar da muke ciki.

Najeriya da Argentina na rukunin daya ne a gasar, kuma za su buga wasan su ne a ranar 26 ga wata Yunin shekarar nan da muke ciki.

Masana harkokin wasanni na ganin cewa Kasar argentina zata nemi daukar fansa kan nasarar da Najeriya ta samu a kanta da ci 4-2 a wasan sada zumunci da suka yi a watan Nowambar shekarar da tagabata.