Jam’iyyar APC ta kafa kwamiti na babban taronta mai zuwa ranar Lahadi

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Jam’iyya mai mulkin na kasa ta APC ta kafa wani Kwamiti mai kunshe da mambobi 68, domin babban taronta, kammar yadda Sakatariyar Jam’iyyar da ke Abuja ta sanar a jiya Lahadi.

Sanarwar ta ayyana gwamnan Jihar Muhammad Badaru a matsayin shugaban kwamitin sai gwamnan Jiar Ondo Rotimi Akeredolu a matsayin mataimakinsa, yayin da Sanata Ben Uwajomogu zai kasance Sakatare kuma Mamba.

Cikin Mambobin kwamitin akwai gwamnoni 10 da wasu ‘yan Majalisun Dokokin kasar nan da kuma manyan jagororin Jam’iyyar.

Gwamnonin sune Rochas Okorocha na Imo da Kashim Shettima na Borno da Aminu Bello Masari na Katsina, sai Abiola Ajimobi na Oyo da Ibrahim Gaidam na Yobe da kuma Nasir El-Rufa’i na Kaduna.

Sauran sun hadar da Simon Lalong na Filato da Bindo Jibrila na Adamawa da Yahaya Bello na Kogi, sai kuma Godwin Obaseki na Jihar Edo, yayin da tsohon shugaban majalisar Dattijai Sanata Ken Nnamani shi ma ya kasance mamba.

‘Yan majalisar dattijan da ke cikin kwamitin su ne Sanata Ahmad Yarima da Adamu Aliero da Danjuma Goje da Abdullahi Adamu, sai George Akume da Ovie Omo-Agege da Andrew Uchendu, sauran su ne Abdullahi Danbaba da Baba Kuka da kuma John Enoch.

Ministoci biyu na cikin kwamitin sun hadar da na Kwadago da nagartar aiki Chris Ngige da takwaransa Neja-Delta Uguru Usani.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO