Freedom Radio Nigeria Labaran Wasanni Tsohon dan wasan kungiyar super eagles ya bukaci mai horas da kungiyar lalubo hanyar atisaye na musssaman

Tsohon dan wasan kungiyar super eagles ya bukaci mai horas da kungiyar lalubo hanyar atisaye na musssaman



Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles  Emmanuel Amunike ya bukaci mai horas da kungiyar Gernot Rohr, da ya lalubo hanyoyin yi wa ‘yan-wasan atisaye na musamman, da zai sa su samu nasara a gasar cin kofin duniya, da zai gudana a kasar Rasha a watan Yuli shekara da muke ciki.

Amunike ya kuma ce, idan akayi la’akari da taka ledar da yan wasan kungiyar ta Super eagles suka yi a wasan sada zumunci da kasashen Serbia da Poland, ya kamata a baiwa yan wasan horo na musamman musamman sabbin salon taka leda, wanda hakan ka iya ba yuwa ga nasarar su yayin gudanar da gasar.

 

A wani labarin kuma, ‘yar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta kasar Amurka Desiree Linden, ta lashe wasan Boston marathon karo na farko tun bayan shafe shekaru talatin da uku kasar bata yi nasara a bangaren ba.

 

Linden mai shekaru talatin da hudu, ta tsallake layin wasan ne cikin hawa biyu da mintuna talatin da tara.

Rahotanni dai sun nuna cewa, Lisa Larsen itace wadda ta lashe wasan tun shekarar 1985.

 

.A wasan da za’a buga a Firimiya Ingila a daren yau

-Brighton & Hove Albion? – ?

Tottenham Hotspur

A seiar Italiya kuwa

Inter? – ? Cagliari

 

A wasanni  laligar Spaniya

Deportivo La Coruna ? – ? Sevilla

Celta Vigo ? – ? Barcelona

Villarreal ? – ? Leganes