Ganin kimar na gaba ne ya sa muka amince da sulhu game da rikicin da ya dabai-baye majalisa-Kabiru Alhassan Rurum

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano Kabiru Alhassan Rurum, ya ce, ganin kimar na gaba shi ya sa suka amince da sulhun da aka yi musu game da rikicin da ya dabai-baye majalisar dokokin a ‘yan kwanakin nan.

Kabiru Alhassan Rurum ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da bangarensa ya gudanar a daren larabar da ta gabata.

Ya ce, tun da farko dama ba su nemi sauyin shugabancin don biyan bukatun kansu ba sai don neman gyara game da yadda ake jagorancin majalisar.

A nasa bangaren Abdullahi Chiromawa wanda shi kadai ne dan majalisa daga jam’iyyar PDP ya ce, duk da cewa ba jam’iyyar sa ce ta sa baki cikin lamarin ba amma ya yi biyayya ga matakin da shugabannin bangaren da yake goyon baya suka dauka na amincewa da sulhun.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO