Freedom Radio Nigeria Labaran Wasanni Kwamitin tsara sabon kundin tsarin mulki zai fara aiki domin gudanar da zaben shugabannin hukumar Kwallon Kwando

Kwamitin tsara sabon kundin tsarin mulki zai fara aiki domin gudanar da zaben shugabannin hukumar Kwallon Kwando

Shugaban hukumar kwallon Kwando ta Najeriya Engr Musa Kida, ya ce nan ba da dadewa ba, kwamitin tsara sabon kundin tsarin mulki zai fara aiki domin gudanar da zaben shugabanni kamar yadda hukumar kwallon kwando ta duniya FIBA ta bukata.

Shugaban hukumar ta NBBF ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki a garin Lagos.

A cewar Musa Kida, idan hukumar kwallon kwando ta duniya ta amince da sabon kundin tsarin mulkin hukumar za ta gudanar da zaben sabbin shugabanni.