0 Comments

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a nan Kano, ta ki amincewa da sakin fasfon din tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau, don bashi damar zuwa aikin Umara na wannan shekara.

Mai shar’ia Zainab Bage Abubakar ce ta furtan hakan, tana mai cewa,  tsohon Gwamnan da kansa ya yi tattaki zuwa kotun, inda ya bukaci kotun da ta umarci mataimakin magatardar kotun ya baiwa Malam Ibrahim Shekarau, fasfon din sa, don samun damar zuwa aikin Ummara na wannan shekara, daga ranar 30 ga watan Mayu zuwa 23 ga watan Yunin da muke ciki, amma kotun ta ki amincewa da bukatar tasa.

Mai shari’a Zainab ta kuma ce, kotun ta kwace fasfon tsohon Gwamnan ne don hana shi tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare.

Hukumar EFCC ce dai ta gurfanar da Malam Ibrahim Shekarau a gaban kotun tare da Aminu Bashir Wali da Mansur Ahmed bisa zargin karkatar da makudan kudade, wanda tsohuwar Ministan man fetur Diezani Alison Madueke ta basu da nufin yin amfani da su a babban zaben shekarar 2015.

Share
Share
Language »