Shugaba Buhari ya bada umarnin sauya mafi yawan jami’an yan sanda Zamfara aiki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin da a yiwa mafi yawa daga cikin jami’an yan sandan jihar Zamfara sauyin wuraren aiki a wani bangare na magance ayyukan yan ta’adda da ke addabar jihar ta Zamfara.

 

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da wakilai da ga majalisar kolin shari’ar addinin musulunci suka kai masa ziyarar a fadar sa da ke Aso Villa a jiya Litinin.

 

Shugaban kasar  ya kuma nuna damuwar a wani bangare na  maida martani kan kashe-kashen da ake yi da kuma tada tarzoma a wasu bangarorin kasar nan.

 

Rahotanni sun yi nuni da cewa a yanzu haka jihar Zamfara na fama da rikicin satar shanu da kuma satar mutane a yan kwanakin nan.

 

A yanzu haka dai yan ta’adda da masu dauke da makamai sun tayar da hankulan al’ummar jihar cikin yan watannin da suka gabata, biyo bayan kisan wadanda basu jiba basu gani ba da kuma kone gidaje da dama.

Share
Share
Language »