Hukumar JAMB ta ce kaso ashirin da biyar cikin dari ne suka samu nassara a jarabawarsu

Hukumar JAMB da ke shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandare ta kasa, ta ce; kasa da kaso ashirin da biyar cikin dari na dalibai da suka rubuta jarabawar UTME a cikin wannan shekara ne kawai suka samu sakamako mai kyau.

 

Shugaban hukumar farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan, yayin wani taron tsara manufofin aiki wanda ya gudana a jihar Osun a jiya Talata.

 

Ya ce, dalibai miliyan daya da dubu dari shida uku da dari daya da tamanin da daya ne suka rubuta jarabawar yayin da dubu dari hudu da goma sha hudu da dari shida da casa’in da shida ne suka samu sakamakon maki sama da dari biyu.

Share
Share
Language »