gwamnonin najeriya sun yi wata ganawa a abuja kan mafi karancin albashi

Gwamnonin kasar nan sun yi wata ganawa a daren jiya a birnin tarayya Abuja wadda suka tattauna batutuwa da suka shafi mafi karancin albashi da rashin tsaro da ke addabar kasa da kuma wasu lamuran da ke alaka da ci gaban kasa.

Rahotanni sun ce ana saran gwamnonin za su kuma gana da shugaban hukumar aikawa da sakonnin ta kasa da kuma attorney Janar kuma kwamishinan shari’a game da batun dagin kasa na bai daya.

Haka zalika yayin taron, za su kuma zanta kan rashin jituwa da ke abkuwa tsakanin bangaren majalisa da kuma na zartaswa.

Kungiyar kwadago ta kasa NLC dai, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta amince da naira dubu sittin da shida a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikata, lamarin da kungiyar gwamnonin ke shakku kan hakan.

Share
Share
Language »