Jami’an DSS sun mamaye majalisar dokoki da safiyar yau

Jami’an tsaro sun mamaye majalisar dokokin Najeriya da safiyar yau Talata.

Jami’an tsaro da suka rufe fuskokin na hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun rufe majalisar dokokin, rahotanni sun bayyana cewa sun isa harabar majalisar ne da misalin karfe 6:00 na safiyar yau Talata.

Jami’an tsaron sun kuma hana ma’aikata da ‘yan majalisar da kuma manema labarai shiga cikin harabar majalisar.

Sai dai daga bisani bayan da ‘yan majalisar suka yi kokarin shiga cikin zauren majalisar, jami’an sun bude kofar bayan da aka yi ta turka-turka a tsakanin su.

Jami’an tsaron na DSS sun dai bude kofar ne da misalin karfe 8:15 yayin da suka kira ‘yan majalisar da su zo su shiga zauren.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO