Wata kotu da ke Abuja ta baiwa sufeton yan sanda damar mika sammacin kotu ga Bukola Saraki

Wata kotu dake yankin Lugbe a birnin Abuja ta bawa babban sufeton yansanda na Najeriya Ibrahim Idris damar sammacin kotu ga Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki.

A wasikar da kotun ta bawa babban Sufeton Yansandan ta hanyar Barrister Oluwatosin ojaomo an nemi babban Sufeton Yansanda da ya mikawa Bukola Saraki tuhumar da ake yi masa data shafi aikata laifuffuka.

Barrister Oluwatosin ya zargi Bukola Saraki da kin mutunata gayyatar da babban sufeton yansandan kasar nan yayi masa ranar 24 ga Watan Yuli na shekarar bana da kuma hana binciken laifuffuka da kuma kin biyayya ga babban jamii dake aiwatar da aikin da doka ta bashi damar yayi wanda yace hakan laifi ne karkashin sashi na 136 da 149 na kundin Penal Code

An saka ranar 10 ga watan Satumba na bana domin fara shariar.

Rundunar yansandan kasar nan ce dai ta gayyaci Sanata Bukola Saraki da yayi mata bayani akan fashi da aka aikata a garin Offa na jahar Kwara a watan Afrilun shekarar da muke ciki inda aka zargi shugaban na majalisar dattijai da Gwamnan jahar Kwara Abdulfatah Ahmad.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO