Jam’iyyar APC ta karyata rade-radin fitar da jadawalin gudanar da zaben cikin gida zaben 2019

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Jam’iyyar APC ta karyata rade-radin da ke yawo cewa ta fitar da jadawalin gudanar da zaben cikin gida na babban zaben shekarar badi.

A baya-bayan nan ne rahotanni ke yawo cewa ta fitar da jadawalin gudanar da zaben cikin gida.

Rahotannin da  jaridar Daily Times ta bayyana cewa Jam’iyyar zata gudanar da zaben cikin gida na yan majalisun dokokin jihohi a ranar 15 ga watan satumba sai kuma ranar 19 ga watan satumba da za’a gudanar da na yan majalisun wakilai sai na sanatoci da za’a gudanar a ranar 23 ga watan na satumba.

Haka kuma za’a gudanar da na gwamnoni a ranar 28 ga watan na Satumba, sai kuma na shugaban kasa a ranar 6 ga watan Octoba.

Jaridar ta kuma bayyana cewa ta samo wannan jadawalin ne la’akari da jadawalin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da ta ce za’a fara zaben cikin gida na jam’iyyu a ranar 18 ga watan Agusta.

Sai dai jam’iyyar ta jaddada cewa ita fa ba ta fitar da jadawalin ba har kawo yanzu.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO