Shugaba Buhari ba ya tsoron amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a-Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ya tsoron amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a wato (Card reader) a yayin babban zaben kasa da za a yi a badi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.

Sanarwar ta ce, ba kamar yadda ‘yan jam’iyyun hamayya da wasu jaridu ke alakanta kin sanya hannu kan kudirin gyaran dokar zabe da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki yi da cewa yana tsoron amfani da na’urar Card reader da kuma kada kuri’a ta na’ura mai kwakwalwa ba, a cewar Garba Shehu, shugaba Buhari ya fi kowa son amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a.

Malam Garba Shehu ta cikin sanarwar dai ya kuma ce batun na’urar Card reader ko kada kuri’a ta hanyar na’ura mai kwakwalwa bai taso daga bangaren zartaswa ko na majalisa ba yayin gyaran dokar zabe a don haka bai ga dalilin da wasu zasu fake da shi wajen tursasa shugaban kasa ya sanya hannu kan dokar zabe da ke cike da kura-kurai ba.

Sanarwar ta kara da cewa batun Card reader lamari ne da aka wuce gun, domin kuwa tun shekarar dubu biyu da goma sha biyar babu wani zabe da hukumar zabe ta kasa INEC ta gudanar ko za ta shirya nan gaba ba tare da na’urar Card reader ba.

Share
Share