Shugaba Buhari ya dakatar da ‘yan sanda daga gayyatar Sanata Ademola

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci sufeto Janar na ‘yan sanda Ibrahim Idris da ya janye gayyatar da ya yiwa dan takarar gwamnan jihar Osun a karkashin jam’iyyar PDP Sanata Ademola Adeleke game da zargin sa da satar jarabawa.

Wata majiya ta shaidawa manema labarai cewa, shugaba Buhari ya shaidawa sufeton ‘yan sandan cewa da su dakatar da binciken da su ke yi har sai bayan an kammala zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 22 ga watan da muke ciki na Satumba.

A jiya Laraba ne dai, rundunar ‘yan sandan kasar nan ta gayyaci Sanata Ademola Adeleke tare da wasu mutane hudu da su gurfana gaban wani kwamitin bincike na musamman a Abuja.

A cewar ‘yan sandan ana zargin su ne da laifin satar jarabawa da hadin baki wajen aikata laifi da kuma yin sojan gona.

Sauran wadanda ‘yan sandan suka gayyata tare da Sanata Ademola Adeleke sun hada da: Mr Sikiru Adeleke da shugaban makarantar sakandiren Ojo-Aro Community Grammar School, Alhaji Aregbesola Mufutau, da wani jami’in makarantar mai rajistar dalibai da ke rubuta jarabawa Mr Gbadamosi Thomas da kuma daya daga cikin malaman makarantar Mr Dare Olutope.

Share
Share