Kotu a Abuja ta umarci wani asibiti ya biya diyyar naira miliyan daya bisa fitar da rahoton bogi

Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja ta umarci wani asibiti mai zaman kansa da ke birnin, da ya biya wani mutum da matar sa, diyyar naira miliyan daya sakamakon sakacin da asitibin ya yi na fitar da rahoton bogi wanda tun farko ya nuna cewa, matar mutumin tana dauke da tagwayen juna biyu.

Tun farko dai wanda ya shigar da karar dmai suna BamikoleOwolabi, ya shaidawa kotun cewa; gwajin juna biyu da asibitin ya yiwa matar sa mai suna Mercy, sakamakon ya nuna cewa tana dauke da tagwaye, sai dai da lokacin haihuwarta ta yi, maimakon tagwaye sai ta haifi ‘Da daya a don haka ya bukaci kotun da ta tursasa asibitin ya biya shi diyya.

Sai dai asibitin ya dage kan cewa, matar ta haifi jariri daya ne mai nauyin kilogram kusan uku da rabi, sannan ya kara da cewa, a kimiyance zai yi matukar wuya a ce a haifi tagwaye kuma nauyin su kilogram kusan uku da rabi.

Da yake yanke hukunci alkalin kotun mai shari’a Jude Okeke ya kama asibitin da laifin sakaci wajen fitar da sakamakon bogi, inda ya bukace hukumomin asibitin da su biya diyyar naira miliyan daya ga BamikoleOwolabi da matar sa.

Share
Share