Hukumar IOM ta ceto tare da dawo da yan Najeriya 9888 daga kasashe daban-daban

Hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya (IOM) ta ce ya zuwa yanzu ta samu nasarar ceto ‘yan kasar nan dubu tara da dari takwas da tamanin da takwas tare da dawo da su gida daga kasashe daban-daban.

Babban jami’in hukumar Frantz Celestin ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai wa hukumar yaki da masu safarar bil’adama ta kasa (NAPTIP) jiya a Abuja.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’ar yada labaran hukumar ta NAPTIP NnekaAniagoh.

Cikin sanarwar hukumar ta (IOM) ta sha alwashin yin aiki tare da hukumar (NAPTIP) domin dakile safarar bil’adama a kasar nan.

Sanarwar ta kuma ruwaito shugabar hukumar yaki da safarar bil’adama ta kasa (NAPTIP) Dame Julie Okah-Donli tana cewa, hukumar tana aiki ba dare ba rana don tallafawa wadanda aka dawo da su daga kasashen ketare don sake dawo da su cikin al’umma.

Share
Share