Kungiyar SERAP ta bukaci shugaba Buhari ya umarci ministan shari’a ya dauki matakin gaggawa kan shari’ar badakalar cin hancin wadanda suka sauka daga mulki

Kungiyar da ke rajin tabbatar da adalci a cikin ayyukan gwamnati da yan majalisu SERAP ta bukaci shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya umarci ministan shari’a kuma attorney Janar Abubakar Malami ya fara daukar matakin gaggawa kan shari’ar badakalar cin hanci da rashawa da ya hadar da gwamnoni masu ci da kuma wadanda suka sauka.

Wannan na kunshe cikin wata wasika da kungiyar ta aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari mai dauke da kwanan watan 5 ga watan Oktoba da ke dauke da sa hannun mataimakin daraktan kungiyar Timothy Adewale.

Ta cikin wasikar kungiyar ta nuna damuwar ta kan yadda ake kawo tsaiko wajen yanke hukuncin kan gwamnonin da aka zarga da cin hanci da rashawa a kasar nan, inda ta ce hakan ba abin da zai haifar sai kara karfafa ayyukan cin hanci da rashawa.

SERAP ta kuma ce abin takaici ne a ce hukuncin wadannan mutane na yin tafiyar Hawainiya, musamman ma gwamnonin da aka zarga da cin hanci da rashawa da halasta kudaden haramun, amma kotuna na jan cikin wajen yanke hukunci duk da an kama su da laifi.

Kungiyar ta ce wasu da ga cikin shari’ar wadanda aka zarga da cin hanci da rashawar da suka hadar da gwamnoni masu ci da wadanda suka yi ritaya anfaro ne tun a shekarar 2007 amma har yanzu kotuna basu yanke hukuncin ba.

Share
Share