Hukumar NDLEA: Sun koka na yadda matasa ke ta’amali da kwayoyin Tramadol

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta koka kan yadda matasan kasar nan da kuma Mata ke ta’ammali da Kwayoyin Tramadol da kuma maganin tari na sha.

Shugaban hukumar ta NDLEA Kanar Muhammad Abdallah mai ritaya ne ya sanar da hakan yayin jawabin da ya gabatar kan yadda za a yaki aikata munanan laifuka gami da shan miyagun kwayoyi a Duniya, a babban taron taron zauren Majalisar dinkin Duniya a birnin New York din Amurka.

Kanar Abdallah mai ritaya ya jaddada kudurin kasar nan wajen mara baya ga tanade-tanaden da kasashen Duniya suka yin a yaki da miyagun laifuka da kuma ta’ammali da muggan kwayoyi.

Ya kara da cewa Najeriya ta sake jan damara wjen kawar da mummunar dabi’ar nan ta safarar mutane da yaduwar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma dakile ayyukan masu halasta kudaden haram.

Share
Share