UNICEF:ya fara shiri na mussama ga masu rike da masarautun gargajiya

asusun tallafa wa yara na majalisar dinkin duniya UNICEF

Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya fara taro na musamman da masu rike da masarautun gargajiya a arewacin kasar nan domin tattauna matsalar yawaitar yara kananan da basa zuwa makaranta.

Wannan ya biyo bayan wani rahoto da hukumar ilimin bai daya UBEC ta fitar da ke cewa sama da yara miliyan 13 ne basa zuwa makaranta a kasar nan.

A cewar UBEC kaso tamanin daga cikin wannan adadi sun fito ne daga arewacin kasar nan, inda kuma kuma asusun na UNICEF ya ce wadannan yara ba a boye suke a cikin al’umma ba ana ganin su suna ta watangaririya a gari.

A cewar shugaban hukumar ta UBEC Dr Hamid Bobboyi ya ce al’amarin na bukatar nazari na tsanaki da kuma sanya hannun dukkanin masu ruwa da tsaki a kasar nan domin magance matsalar

A nasa jawabin mataimakin daraktan asusun na UNICEF a Najeriya Pernille Ironside ya ce asusun na UNICEF ya fahinci irin muhimmancin da taron ke da shi da kuma irin rawar da masu rike da saurautun gargajiya ke takawa musamman ma a arewacin kasar nan wajen wayar da kan jama’a

 

A don haka asusun ya ci alwashin yin aiki da su domin kawo gywara a cikin al’amarin.

 

Share
Share