Shugaba Buhari yayi ganawar sirri da jagoran jam’iyyar APC

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Shugaban kasa Muhammadu Buharin ya yi ganawar sirri da jagoran jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu a jiya Laraba a fadar sa da ke Abuja.

Jagoran jam’iyyar ta APC Asiwaju Bola Tinubu ya isa fadar shugaban kasa da misalign karfe 4 na yammacin jiyan.

Sai dai kawo kammala ganawar sirrin a jiya ba’a bayyana wa manema labarai mainene makasudun ganawar ta su ba.

Amma kuma ana hasashen cewar ganawar ba zata rasa nasaba da shiga tsakani da shugaban kasa Muhamamdu Bauhari yayi kan rikicin da ‘ya’yan jam’iyyar ta APC suka fada tun bayan kammala zaben fidda gwani a sassan kasar nan.

Rahotanni sun bayyana cewar, ganawar ta su ta dauki lokaci, kuma ya zo dai-dai da kasa da awanni 24 da shugaban yayi liyafar cin abincin dare da ‘yan takarar da aka batawa a yayin zaben na fidda gwani.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO