Kamfanin NNPC ya bayyana tabbacin cewar yana da ishasshen man fetur

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Kamafanin main a kasa NNPC ya baiwa masu ababen hawa tabbacin cewa yana da isasshen Man fetur da dangoginsa da za su isa ga jama’a, duk da yunkurin Kungiyar Kwadago ta kasa NLC na tsunduma yaji aikin sai baba ta gani a gobe Talata.

Wannan tabbaci na fitowa ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin Ndu Ughamadu ya bayar jiya a Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa Kamfanin ya na da isasshen Man Fetur da albarkatunsa za a samarwa al’umma na tsawon kwanaki 39, a don haka babu wani abin damuwa dangane da barazanar karancinsa.

Ndu Ughamadu ya shawarci jama’a musamman masu ababen hawa da ka da su firgita ballantana su shiga saye tare da tara Man a gidajensu.

Sannan ya bukaci a gaggauta sanar da su da zarar an samu wani gidan Mai da ke yunkurin boye Man ko kuma aikata wani abu da ya sabawa doka.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO