Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta kama mutane 35 bisa zargin su da hannu a rikicin jihar

Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba tace mutane talatin da biyar ta cafke da ake zargin su da hannu wajen kitsa rikicin da ya kunno kai jihar a baya-bayan nan.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar ASP David Misal, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, lokacin da yake ganawa da manema labarai a Jalingo babban birnin jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa a baya-bayan nan ne wasu ‘yan bangar siyasa suka tayar da wani rikici a Jalingo babban birnin jihar ta Taraba, lamarin da ya sanya rundunar ‘yan sandan jihar ta baza jami’an ta.

A cewar ASP David Misal rikicin ‘yan bangar siyasar da ratsa ta kasuwar Jalingo yayi sanadiyyar konewar shaguna da dama, lamarin da ya sanya rundunar tayi gaggawar tura jami’an ta, sai dai kafin suka wurin tuni shaguna da dama suka kone kurmus.

Ya kara da cewa rundunar ba zata yi kasa a gwiwa ba, wajen cigaba da farautar duk wanda ake zargi da hannu wajen tayar da rikcin, tare da daukar tsauraran matakai a kan sa.

Jami’in hulda da jama’r na rundunar ‘yan sandan jihar ta Taraba, ya kuma ja hankalin matasa, da su nesanta kan su daga duk wani abu da ka iya tayar da hankulan jama’a.

ASP David Misal ya ce wadanda rundunar ta cafke zata mika su gaban kotun da zarar sun kammala bincike a kan su.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO