Month: May 2019

CP Ahmed Iliyasu ya zama kwamishinan yan sandan Kano

Babban sefeton ‘yan sanda na Najeriya Muhammadu Adamu ya bada umarnin da a gaggauta mayar da kwamishinan ‘yan sanda Ahmad Iliyasu zuwa jihar Kano a matsayin sabon kwamishina  bayan da wa’adin aiki na CP Wakili Mohammed ya kare. A ranar 26 ga watan da muke ciki ne wa’adi aikin kwaminan ‘yan sanda Wakili Mohammed ya […]

Hukumar NYSC ta gargadi Hukumomin Jami’o’in Najeriya

Hukumar kula da masu yiwa kasa hidima ta kasa NYSC, ta gardadi hukumomin jami’o’in kasar nan da su guji tura dalibai zuwa bautar kasa, da suka saba ka’idojin ta. Daraktan Janar na Hukumar Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ne ya bayyana haka, a wani taron karawa juna sani a birnin tarayya Abuja, da ya gudana a […]

Shugaba Bahari ya soki Shugabannin dokokin tarayya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Shugabannin majalisun dokokin tarayya Sanata Bukola Saraki da Yakubu Dogara a matsayin wadanda ke da karancin kishin kasa. Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke hira ta musamman da gidan talabijin na NTA a daren jiya. A cewar shugaba Buhari ko kadan bai ji dadin halayyar […]

UBEC: akwai Malamai dayawa da basuda kwarewar aiki

Hukumar kula da ilimin bai daya ta Najeriya UBEC ta ce kaso 57 na malaman makarantu a Najeriya ne suke da kwarewar aiki. Shugaban Hukumar ta Dr Hamid Bobboyi ne ya bayyana haka a Kaduna lokacin da ya ke gabatar da wata mukala mai taken matsayin ilimi a jihar Kaduna. Ya ce an samu karuwar […]

Aisha Bahari ta soki shirrin Gwamnatin tarayya na rage fatara

Mai dakin shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari, ta ce, shirin gwamnatin tarayya na rage fatara da samar da aikin yi ga matasa  bai samu nasara ba a yankin arewacin kasar nan. Uwargidan shugaban kasar ta bayyana hakan ne lokacin da ta ke tattaunawa da mata a fadar Asorok da ke Abuja a jiya Asanar. A […]

‘yan sanda sun gano wurin ake hada makamai a Benue

Rundunar yan sanda a jihar Benue ta kara gano wasu gurare da ake hada muggan makamai a yankin Ikache dake karamar Hukumar Oju inda aka kama wani mai suna Orohu Akodi mai shekaru Talatin da bakwai wanda shine mamallakin gurin. Kwamishinan yan sandan jihar ta Benue Mr Garba Mukaddas ne ya tabbatar da hakan, inda […]

Kungiyar ASUP ta janye yajin aikin da ta shirya farawa

Kungiyar malaman kwalejojin kimiyya da fasaha ta kasa ASUP reshen kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano, ta janye shirin fara yajin aikin mako guda da ta shirya za ta fara a jiya Alhamis. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Dr. Ahmad Zubair Chedi. Sanarwar ta ce […]

Gwamnatin tarayya ta yi karin girma ga jami’ai 18,954

Gwammatin tarayya ta yi Karin girma ga jami’an tsaro na Civil Defence, da jami’an hukumar kashe gobara, da ma’aiktan hukumar kula da gidajenn yari da kuma jami’an hukumar kula da shige da fice su18,954  guda Dubu goma sha takwas da dari tara da hamsin da hudu. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke […]

Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 2 a fadowar ginin Anambra

Rundunar yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da mutuwar mutane biyu sakamakon fadowar wani gini a yammacin jiya laraba a garin Onitsha. Mai magana da yawun rundunar, Haruna Muhammad ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a AwKa babban birnin jihar. A cewar sanarwa, ginin da ke lamba 9 a […]