Author: Baraka Bashir

Shugaba Buhari ya bada umarnin tsas-tsaura matakan tsaro a jihar Borno

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin daukar tsas-tsauran mataki kan ‘yan ta’adda, sakamakon kisan gillar da ake zargi ‘yan Boko Haram sun yi ga wasu masu gudanar da jana’iza guda sittin a jihar Borno. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa […]

Fadar shugaban kasa ta haramta ayyukan kungiyar ‘yan uwa musulmi

Fadar shugaban kasa ta ce, haramta ayyukan kungiyar ‘yan uwa musulmi wato Islamic Movement in Nigeria, ba ya nufin haramta addinin Shi’a kwata-kwata a kasar nan.   Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.   Malam […]

Babban Jojin Najeriya ya sha alwashin yaki da cin hanci da rashawa

Babban Jojin Najeriya Tanko Muhammad ya lashi takobin yaki da duk wani nau’i na cin hanci da rashawa da ke cikin hukumar shari’ar kasar nan. Tanko Muhammad ya shaida hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da shi jiya […]

WHO:Najeriya na daf da fita daga jeren kasashen masu cutar shan-inna

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce nan ba da jimawa ba za ta ayyana Najeriya a matsayin kasar da babu cutar shan-inna wato Polio. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labaran hukumar a Najeriya Mr Charity Warrington ya fitar jiya a Abuja, a madadin babban jami’in hukumr a kasar […]

Rundunar sojan Najeriya ta harbe yan bindiga 78 a watan jiya

Dakarun Sojin Najeriya na rundunar Operaion Hadarin Daji sun sanar da cewa sun samu nasarar harbe ‘yan bindiga 78 tsakanin watan jiya zuwa na Yulin nan da mu ke ciki. Haka kuma rundunar ta ceto mutane 50 da aka yi garkuwa da su sannan suka kwato bindigogi 47 kirar AK47 da bindiga 1 mai sarrafa […]