Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Cibiyar CITAD ta ja kunnen fasinjoji kan kula da kayan su a filayen jirage

Published

on

Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma, CITAD ta yi kira ga fasinjojin jirgin sama da su rinka isa filin jirgin sama kan lokaci don samun damar auna kayansu cikin lokaci tare da sanya ido sosai kayan kayan nasa don gujewa sanya musu kayan matsala.

Jami’in gudanarwar na cibiyar, Malam Isah Garba ne ya bayyana haka yau a wajen taron manema labarai da cibiyar ta gudanar a nan Kano.

Malam Isah Garba ya ce la’akari da yadda aka zargi wasu jami’ai a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da sanya kwaya a kayan wata fasinja, akwai bukatar matafiya su rinka kula sosai.

Cibiyar ta kuma bukaci hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA da ta ci gaban da sanya ido soasai da nufin tabbatar da ba a sake sanya wa wani kwaya a kayan wani.

Cibiyar ta kuma jaddada bukatar a hukunta duk wanda aka kama da laifin cusa kwaya a kayan matafiya a filin jirgin Malam Aminu Kano kasancewar kotu ta bada belin su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!