Connect with us

Kaduna

Garkuwa da mutane: An sace ɗaliban sakandire a Jihar Kaduna

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari makarantar Saint Albert College Kagoma, dake ƙaramar hukumar Jama’a a ranar Litinin, inda sukayi awon gaba da dalibai uku.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Muhd Jalige ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata.
Ya kuma ƙara da cewa, daga shigar ƴan bindigar harabar makarantar ne suka fara harbe-harbe, inda suka raunata wasu ɗaliban tare da yin garkuwa da guda uku.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan ya yabawa mutane, musamman yadda suke baiwa rundunar rahotannin sirri wanda yake taimaka musu wajen gudanarda ayyukan magance matsalar rashin tsaro a jihar Kaduna.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!