Connect with us

Labarai

Majalisar dokoki ta buƙaci gwamnatin Kano ta gyara filayen wasanni

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano, ta buƙaci gwamnatin jihar da ta gyara filin wasa na Kano Pillars da ke unguwar Sabon Gari da na Sani Abacha a Ƙofar Mata.

Buƙatar gyaran na su ta biyo bayan ƙudurin haɗin gwiwa da ƴan majalisar da suka haɗar da wakilin ƙaramar hukumar Ƙaraye Alhaji Nasiru Abdullahi Dutsen Amare da takwaransa na ƙaramar hukumar Rano Alhaji Nuraddeen Alhassan Ahmad suka gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba.

Da yake gabatar da ƙudurin Alhaji Nuraddeen Alhassan Ahmad wanda shi ne shugaban Kwamitin harkokin wasanni na majalisar ya ce, gabatar da ƙudurin ya biyo bayan yadda filayen wasan suka lalace.

Har ma yace, lalacewar ta su zai sanya jihar Kano ta samu koma baya ta fannin wasanni.

Haka kuma a zaman majalisar, ta karɓi rahoton kwamitin haɗin gwiwa tsakanin kwamitocin majalisar da suka haɗa da kwamitin karɓar ƙorafe-ƙorafe da na Ilimi da kuma kwamitin harkokin ƙasa, kan ƙorafin da ƙungiyar iyaye da malaman Makarantar Izazuddin da ke unguwar sani mai Nagge suka gabatar.

Da yake gabatar da rahoton, shugaban Kwamitin Alhaji Umar Musa Gama, mai wakiltar ƙaramar hukumar Nassarawa ya ce, binciken su ya gano cewa filin na magada ne, saɓanin yadda wasu ke cewa mallakin al’ummar yankin ne.

Sai dai bayan bada gudunmawar tsokaci ne daga mambobinta, majalisar ta amince da rahoton.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Archives