Connect with us

Addini

Na janye ƙara, amma na bar wa Allah – Farfesa Maƙari

Published

on

Babban limamin ƙasa da ke Abuja Farfesa Ibrahim Maƙari ya sanar da janye ƙarar da ya shigar da Dr. Abdallah Usman Gadon ƙaya, sai dai ya ce ya bar wa Allah al’amarin.

Da yake zantawa da Freedom Radio, Farfesa Maƙari ya ce, ya janye ƙarar ne, sakamakon saka bakin magabatansa, ciki har da mahaifinsa.

Ya ce, dama an shigar da shari’ar ne a kotuna guda biyu, babbar kotu da kuma kotun shari’ar musulunci.
Amma kawo yanzu lauyoyinsa na ƙoƙarin janye ƙarar.

Farfesa Maƙari ya ƙara da cewa, ya barwa Allah, game da cewa ana da muryarsa yana kiran waya yana kare masu ɓatanci, kuma har yanzu yana ƙalubalanta kan a fito da muryar a cewarsa.

A ƙarshe ya yi kira ga ɗalibansa da ransu ya sosu, kan su yi haƙuri game da wannan matakin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!