Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Sharhi

Sharhi: Akwai bukatar a samar da tsarin tallafawa ‘yan kasuwa domin su farfado

Published

on

A yanzu dai maganar da aka mayar da hankali a kanta ita ce irin matakan da ya kamata a bi don tallafawa jama’ar da ke gudanar da harkokin kasuwanci da sauran al’amura yadda za su murmure daga dogon lokacin da suka dauka suna zama a gida sanadiyyar cutar corona.

A baya- bayan nan Shirin da gwamnatin tarayya ta yi na sake dawo da harkokin tattalin arziki da sauran al’amuran kasuwanci a kasar ya fara, kasancewar ta sassauta dokar da ta hana hakan.

Ta cikin sanarwar ta ce gudanar da harkokin tattalin arzikin kuwa ta fito ne daga bakin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ranar Litinin 1 ga wannan wata na Yuni a wajen taron manema labarai na yau da kullum da kwamatin shugaban kasa kan dakile cutar corona ke shiryawa.

Duk da wannan sassauci da gwamnatin tarayyar ta bayyana kan harkokin tattalin arzikin, kulle kan kai-da-komon jama’a daga wannan jiha zuwa wacan na nan daram.

A lokacin wannan taron manema labarai, Boss Mustapha ya kuma sanar da sassauta dokar zaman gidan da gwamatin tarayya din ta dora a kan jihar Kano.

Watakila saboda irin kosawar da jama’a suka yi zaman gidan da suka dade suna yi kuma ya sanya kashegari jama’a da dama suka fito don isa guraren sana’o’insu, bayan kuma a dokar zaman gida da gwamnatin jihar Kano ta saka ranar Talata bata daya daga cikin ranaku uku da aka ware don jama’a su fita su gudanar da harkokin ci gaban tattalin arzikinsu.

Ranakun da gwamnatin ta jihar Kano din ta ware don hakan dai sune Juama’a, Lahadi da kuma Laraba na kowane mako.

Sai dai kamar yadda muka ambata, watakila zakuwa da su koma harkokin kasuwancinsu ya sanya mutane musamman a babban birnin jiha suka fito don tafiya wajen harkokinsu.

Sai dai su kuma jami’an tsaro da aka baiwa alhakin tabbatar da jama’ar sun bi wccan doka sai suka fito suka tattare hanyoyi don hana mutane kai-da-komo kamar yadda aka ba su umarni.

Wannan lamari ya jawo cece-kuce mai yawa tsakanin jami’an tsaron da jama’ar da suka fito don tafiya wajen harkokin neman arzikinsu a gurare daban-daban na birnin Kano.

An yi sa’a dai ba a yi wata batacciya ba sanadiyyar wannan lamari don kuwa ubangiji Ya kare faruwar hakan.

Ko ba komai dai irin wannan kiki-kaka ta fito da halin matsi da jama’a suke ciki karara kasancewar tsawon lokacin da suka dauka suna zaune a gida kamar yadda gwamnati ta umarcesu da yi da nufin dakile yaduwar cutar corona da ta miskili duniya baki daya tun daga karshen shekarar da ta gabata har zuwa wannan lokaci.

Ko ba komai dai, matakan da aka dauka na dakile yaduwar cutar ta corona musamman wadanda suka da hana cakuduwar jama’a a guri daya da kai-da-komonsu da sauransu sun yiwa tattalin kasashen duniya illa mai yawan gaske ta yadda wasu masana tattalin arziki suka ce za a dade ana fama da irin sakamakon barnar da ta haifar

Sai dai, al’amarin da ya yiwa tattalin arzikin kasashen da manyan kamfanonin kere-kere da makamantansu na duniya illa ina ga sauran kananan kasashe musamman namu da ke nahiyar Afirka da dama a iya cewa, ‘Yaya lafiyar kura?’

Kasashen mu na Afirka da dama mafi yawansu kullum suna kan layin neman tallafi ne, a ka san za a sha wuya matukar gaske, don corona ta sanya al’amura a duniyar yau sun zama ‘gobarar bera’, watau kowa ta kansa yake yi, don haka mai neman taimako ba shi ga tsuntsu ba shi ga tarko kenan.

Ba tantama, wahalar da jama’a suka shiga ne sanadiyyar zaman gida ya sanya wasu kasashe suka bullo da shirin tallafawa jama’arsu ta hanyoyi da dama da nufin magance musu shiga halin kaka-ni-kayi.

Akwai kasashe da suka dunkuli ruwan kudi suka baiwa jama’arsu, wasu kuma suka dauki gabarar biyan jama’ar tasu duk wata asara da suka yi a harkokin kasuwancinsu sanadiyyar hana su fitar da gwamnatocin nasu suka yi.

Ko muma nan, gwamnatin tarayya ta yi wata hobasa, inda ta nuna za ta daukewa wasu kamfanoni haraji na tsawon wasu lokuta da nufin tallafa musu farfadowa daga magagin kullen corona.

A gaskiya wannan al’amari ne mai kyau daya kamata a aiwatar da shi bilhakki ga dukkan irin wadannan masana’antu na kasar nan wadanda dama dai sun dade cikin matsin tattalin arzikin da kai wasu daga cikin su rufewa.

Shekaru Goma Sha Shida Kenan Cif Da Kafa Kamfanin Da Yafi Nigeria Arziki

Siyasar Kano: Ina makomar Farfesa Hafizu Abubakar?

Sai dai wani hanzari, ba gudu ba, shine irin wannan mataki na yafewa manyan kamfanoni biyan haraji na wani dan lokaci lallai ya hada da   dukkan mai gudanar da kowace irin sana’a a kasar nan komai kankantarta.

Don haka gwamnatoci a dukkan matakai, tarayya, jiha da kuma kananan hukumomi su tabbata ba su karbi kowane irin haraji ko abin da mu a nan muke kira ‘revenue’ daga jama’a zuwa akalla watanni biyu da nufin ba su damar su dan murmurewa tukunna.

Wannan kuwa ya hada har da kasuwanni da tashoshin mota da duk guraren da jama’a ke gudanar da harkokin neman abincinsu da ma irin kudaden ka’ida da kungiyo ke karba daga mambobinsu.

Tuni dai wata karamar hukuma daga cikin kananan hukumomin 44 na jihar Kano ta yiwa jama’arta irin wannan sassauci nawatanni biyu da nufin tallafa musu su dan murmure tukuna.

Lallai ne ita gwamnatin jihar Kano da sauran kananan hukumomin jihar da sauran kananan hukumomin kasar nan da jihohin baki daya da ita kanta gwamnatin tarayya su yi koyi da wannan karamar hukuma wajen sassautawa ‘yan Najeriya su murmure daga matsin da cutar corona ta sanya su a ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!