Connect with us

Labarai

Zargin Almundahana: Ƴan Karota sun kai Baffa ƙara ICPC

Published

on

Wasu jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, sun maka Baffa Babba Dan Agundi gaban hukumar ICPC

Jami’an hukumar sun shigar da korafi ne  bisa zargin Baffa Babba Dan agundi da al’mundahanar maƙudan kuɗaɗe.

Shugaban hukumar shiyar Kano Alhaji Ibrahim Garba kagare ne ya tabbatar da hakan ga Freedom radio.

Kagara ya ce jami’an sun shigar ta ƙarar ne ta cikin wata takarda mai taken “ƙorafi akan shugaban KAROTA bisa aikata almundahana’’.

“masu ƙarar sun bayyanawa hukumar mu cewa tun lokacin da Baffan ya fara jagorantar hukumar ta su, ya fito da wasu sabbin  rasitai na boge, a shiyyoyin da jami’an hukumar ke gudanar da ayyukansu, inda ake karbar masa kudade”.

Ya ci gaba da cewa jami’an sun zargi Baffa Ɗan agundi da baiwa wani dan uwansa mai suna Shehu aikin kula da hada hadar rasitan na boge, wanda kuma ba ma jami’in hukumar ba ne, kuma ma ba ma’aikacin gwamnatin ba ne.

Masu ƙarar sun  kara da cewa, dan uwan Baffan mai suna Shehu, ya dakatar da ayyukan kotun tafi da gidanka da ke ofisoshin shiyya na KAROTA tare da dakatar da aikin ma’aikatan hukumar tattara haraji ta jihar Kano.

Sai dai shugaban hukumar ICPC Ibrahim Garba Kagara ya ce za su bibiyi lamarin domin gano gaskiya.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!