Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Ƴan kasuwa sun kai koken gwamnati ga Alhaji Aminu Alhasan Dantata

Published

on

Ƴan kasuwar Kantin Kwari sun kai kokensu  ga Alhaji Aminu Alhasan Dantata kan ya sanya baki bisa shirin gwamnatin Kano na gina shaguna akan titin Ta’ambo dake kasuwar.

A wata ziyara da ƴan kasuwar suka kai kaiwa attajirin domin neman mafita kan matsalolinsu karkashin jagorancin Alhaji Balarabe Usman.

Da yake bayani Alhaji Balarabe Sa’idu ya ce”Ƴan kasuwa muna buƙatar agajin ka a matsayin ka uba a jihar Kano”.

Da yake nasa Jawabin Alhaji Aminu Alhasan Dantata ya ce “zan baiwa gwamnti shawara kan matsalolin ku don samun mafita, sai dai ina buƙatar ku ci gaba da yin biyayya ga gwamanti domin wanzar da zaman lafiya a cikin kasuwar da ma jihar Kano baki daya”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!