Labarai
Gwannatin tarayya ta gargadi Atiku
Gwamnatin tarayya ta gargadi tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da jam’iyyar sa ta PDP da su daina kada gangar yaki.
Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammed ne ya yi wannan gargadin yayin zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a Abuja.
A cewar sa tsarin adawa irin ta jam’iyyar PDP babu abinda ya ke janyowa sai barazana ga daurewar mulkin dimukuradiya.
Alhaji Lai Muhammed ya ce a tarihin Najeriya babu wani lokaci da aka taba ganin wata jam’iyya da dantakarar da suka manta da muradun kasa suna neman mulki ko mutu ko a yi rai kamar PDP da Atiku Abubakar.
Ministan yadda labaran ya ce suna sane cewa a duk wayewar garin Allahi PDP da Atiku Abubakar suna bullo da sabbin dabaru na yin zagon kasa ga ci gaban kasar nan.
Sai dai da ya ke mai da martani tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya musanta zargin, yana mai cewa babu kanshin gaskiya kan zarge-zargen da gwamnatin ke yi akansa.
A cewar sa, ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammed mutum ne marar gaskiya da ba za a amince da bayanan sa ba, inda ya kuma bayyana gwamnatin Buhari a matsayin na kama karya.