Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

DA DUMI-DUMI: Sadio Mane ya lasher kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afrika

Published

on

An bayyana sunan dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dan kasar Senegal Sadio Mane a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afrika na shekarar 2019.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF Ahmad Ahmad ne ya bayyana Mane a matsayin wanda ya lashe kyautar a yayin babban taron hukumar da ya gudana a kasar Masar.

Sadio Mane ya doke mai rike da kambun Muhammad Salah dan kasar Masar da Riyad Mahrez dan kasar Algeria wajen lashe kyautar.

A shekarar 2019, Mane ya jefawa Liverpool kwallaye 34 tare da taimakawa aka zura 12 wanda hakan ya taimakawa Liverpool lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.

Haka kuma Sadio Mane ya jagoranci kasar sa ta Senegal zuwa wasan karshe a gasar cin kofin Afrika inda suka yi rashin nasara a hannun kasar Algeria da ci daya mai ban haushi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!