Connect with us

Kiwon Lafiya

Bikin ranar mata a karamar hukumar Gaya da Kumbotso

Published

on

A yayin da ake bikin ranar mata ta duniya , kungiyar mata masu wayar da kan  alumna akan harkar lafiya a Kano  wato VCM net sun bi  sawun takoririn  su na duniya wajen gudanar da bikin ranar ta hanyar nuna muhimmacin mata.

 

Kungiyar dai ta shirya  taron fadakar da mata kan ‘yanci su,lafiya su, da tsabtar  muhali su

 

Ta  gudanar da taron  ne a kanana hukumomin Gaya da  Kumbotso

 

Da yake ke jawabi  a Karamar hukumar  Kumbotso jakada Wayar da ka al’umma na hukumar UNICEF  jarumin  a masana’antar Kannywood   Ali nuhu yayi Kira ga mata  da su yi tsayin daka wajen zama jakadu na gari a tsakani iyalan  su

 

Tarurunka biyu sun samu halartar Manya baki da suka hadar da shugaban cibiyar Karta kwana kan yaki da cutar shan ina Dr imam Wada Bello, sai wakilin UNICEF  Mr Farhat Mahadi, dagacin unguwar Mariri da mata wadanda ake bikin dominsu

 

A dai yi amfani da wannan rana wajen gudanar riga-kafin cutar shan inna a  karamar  hukumar Gaya

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,401 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!