Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abincin Naira 30 ya jawo cecekuce.

Published

on

 

A kwanakin nan ministan ayyukan gona Alhaji Sabo Nanono yace a Najeriya, ba’a yunwa kuma abincin Naira talatin ya ishi dan Najeriya yaci ya koshi.

Wannan Magana da Minista Sabo Nanono yayi ta sa ‘’yan Najeriya musamman anan Kano sun shiga kafar Sada zumunta ta Social Media ana ta sukar Ministan na aikin gona.

Yan Najeriya dai sun dade suna kalubalantar Gwamnati game da matsi na tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta da tashin farashin kaya.

Maganar ta Minstan na aikin gona ta kai ga al’ummar kasar nan a kafafan sada zumunta na dakko hotunan abinci suna sakawa inda suke alakanta maganar ta Ministan na noma da kudin da ya kayyadewa yan Najeriya cewa abincin Naira talatin ya ishe su su ci su koshi.

Bayan haka maganganun na ministan noma ya jawo habaici iri daban daban a game da maganar da yayi ta abincin Naira talatin.

Ko a kwanakin nan ma ,sai da Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kara harajin kayayyaki wanda hakan ta sa ake ganin za’a samu tashin goron zabi na kayayyakin masarufi a fadin tarayyar Najeriya.

Tun hawan Shugaba Buhari ne dai kayyaykin masarufi da na rayuwar yau da kullum  suka rika tashin goron zabi wanda hakan yasa ka ‘’yan Najeriya ke ta korafin cewa rayuwarsu ta yi ,musu wahala.

Ko a shekarar 2016 akwai malamin da ya fadawa mahalatta sallar Jumaa cewa ana shan wahala a Najeriya inda ya bayar da misali da wata mata da taje wani gida satar tuwo ,da mai gidan ya biyo ta da miya kafin aje sun cinye tuwon.

Irin wadannan misalan akwai su da dama a korafe korafe na yunwa da yan Najeriya ke fuskanta.

Bayan haka kuma wasu abubuwan da ake korafi da su, shine barace barace da ya karu na magaidanta da mata a tituna da manyan kantuna na nan birnin Kano, inda itace mahaifar ministan na aikin gona Alhaji Sabo Nanono.

Barace baracen mata masu aure da ‘’ya ‘’yan nasu a  gurare da dama a birnin na Kano ana ganin hakan na alaka da matsin tattalin arziki da Gwamnatin tarayya ba ta yiwa ‘’yan najeriya sahihan bayani ba.

Ko sanda Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hau karagar mulki babban kudin da ‘’yan Najeriya suke canji da shi a kasashen waje wacce itace Dalar Amurka daga dari da tamanin ta koma fiye da dari uku da sittin wanda hakan ya saka aka samu hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.

Wannan Magana ta Sabo Nanono wanda shine ministan noma ‘’yan Najeriya da dama  basu dauke ta da wasa ba.

Tunda ana ganin ministan noma shine zai iya gayawa yan Najeriyar gaskiyar halin da kasa take ciki a game da harkokin tattalin arziki da al’amura na abinci.

Ko a kwanannan ma sai da wasu ‘’yan jaridu anan birnin Kano suka binciki wata mai sai da dambu, ko akwai na Naira talatin da mutum zai ci ya koshi, sai tace babu.

Hakan dai ta sa jama’a suna ta kididdiga akan maganar Minista Sabo Nanonono cewa ko abincin Naira talatin zai kosar.

Yaya jamaa ke cigaba da kallan maganar ta minister sabo Nanonon lokaci ne kadai zai bayyana.?

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!