Connect with us

Labarai

Abinda yasa Jamb ta tilastawa dalibai amfani da lambar NIN

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB ,ta ce a bana babu dalibin da zai rubuta jarrabawar shekara 2020 har sai yana da lambar katin dan kasa wato NIN.

Mai Magana da yawun hukumar Dakta Fabian Benjamin ne ya bayyana haka a jiya Talata a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Lagos.

Fabian Benjamin ya ce manufar shi ne samun cikakkun bayanan dalibi a wani mataki na dakile satar jarrabawa.

Yace hukumar ta JAMB ta yi tsarukan da suka kamata da hadin gwiwar hukumar da ke kula da mallakar katin dan kasa domin samun nasarar al’amarin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,845 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!