Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An cafke matar aure na yunkurin shiga da waya gidan gyaran hali

Published

on

Jami’an kula da gidan gyaran hali a jihar Kano sun samu nasarar kame wata matar aure lokacin da take yunkurin shiga gidan da nufin ziyara tare da baiwa kaninta wayar salula samfurin Android bayanda kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Ita dai wannan matar aure mai suna Mariya Iliyasu mazauniyar unguwar Gwanmaja da ake zargin ta da yunkurin shiga gidan gyaran hali na Kurmawa da yammacin jiya Laraba.

Jim kadan bayan ta shiga hannu ne ta bayyana nadama, inda take cewa tabbas zargin da ake mata gaskiya ne.

Musbahu Lawan Kofar Nasarawa shi ne mai magana da yawun ma’aikatan gidan ajiyar da gyaran hali a nan Kano ya bayya cewa da zarar sun gama binciken su zasu mika ta ga rundanar ‘yan sanda domin fadada bincike akanta.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!