Connect with us

Labarai

An nada shugabar riko ta ma’aikata tarayya

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Dakta Folashede Yemi-Esan a matsayin mai rikon mukamin shugabar ma’aikata ta tarayya.

Dakta Folashade Yemi Esan ta maye gurbin Winifired Oyo-Ita wadda ke fuskantar tuhuma sakamakon zargin ta a badakalar sama da naira biliyan uku.

Hakan na kunshe na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai a ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey.

Sanarwar ta ce an bukaci Winifired Oyo-Ita da fara hutu domin bai wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC damar gudanar da bincike kan zargin da ake yi mata.

A cewar sanarwar sabuwar mai rikon mukamin shugabar ma’aikatan tarayyar, Folashade Yemi-Esan wadda ita ce babbar sakatariya a ma’aikatar albarkatun man fetur za ta ci gaba da rike mukamin har zuwa lokacin da za a nada cikakken shugabar ma’aikatan tarayya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,921 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!